Isa ga babban shafi

'Yan ci rani 23 sun mutu yayin kokarin shiga Spain da karfin tsiya

Jami'an Morocco sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon yunkurin da 'yan ci-rani 'yan Afirka suka yi daga arewacin kasar na shiga yankin Melilla na Spain da karfin tsiya ya kai mutane 23.

Yadda aka rika arrangama tsakanin bakin-haure kusan dubu 2000 da suka yi kokarin shiga Spain da kartsin tsiya daga arewacin kasar Morocco.
Yadda aka rika arrangama tsakanin bakin-haure kusan dubu 2000 da suka yi kokarin shiga Spain da kartsin tsiya daga arewacin kasar Morocco. AP - Javier Bernardo
Talla

Da farko dai jami'ai sun ce mutane biyar suka mutu, a lokacin da bakin-haure kusan 2,000 galibinsu 'yan Afirka daga kudu da Sahara suka tunkari kan iyakar kasar Morocco da Spain, da safiyar Juma'a.

Wani jami'in kasar Morocco daga garin Nador da ke kusa da kan iyaka ya ce jami'an tsaro 140 da bakin-haure 76 suka jikkata yayin arrangamar da suka yi, a lokacin da suke yunkurin tsallaka kan iyakar, zuwa cikin Spain.

Yayin da yake bayyana bacin ransa kan aukuwar lamarin, Fira Ministan Spain ya bayyana tururuwar da bakin bakin-hauren suka yi cikin yankin Melilla daga Morocco a matsayin hari da aka kai wa ‘yankin kasar Spain, yayin da masu rajin kare hakkin bil’adama suka bukaci a gudanar da bincike.

Fiye da mutane 500 ne suka yi nasarar shiga yankin dake kula da kan iyaka bayan yanke katangar wayar da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.