Isa ga babban shafi
Rasha - Ukraine

Kotun Ukraine ta yanke wa sojan Rasha hukuncin daurin rai-da-rai

Wata kotu a Ukraine ta yanke wa wani sojin Rasha hukuncn daurin rai-da-rai a jiya Litinin, bayan da ta same shi da laifin kashe wani farar hula, hukunci irinsa na farko tun da da Rasha ta mamaye kasar watanni 3 da suka wuce.

Sojin Rasha, Vadim Shishimarin,dda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai a Ukraine.
Sojin Rasha, Vadim Shishimarin,dda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai a Ukraine. REUTERS - STRINGER
Talla

Hukuncin na zuwa ne a yayain da shugaba Volodymyr Zelensky  ya bukaci ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa da ke halllatar taron tatalin arziki na duniya su yanke huldar cinikayya da Rasha, kana su ci gaba da samar da kasarsa makaman yaki.

Rasha ta yi ta ci gaba da haren harenta a gabashin Ukraine  kamar yadda ta fara makonni 4 da suka wuce, amma hankula sun koma birnin Kyiv, don ganin yadda za ta kaya a tuhumar da ake wa sojin Rasha mai shekaru 21, Vadim Shishimarin.

Sojan mai mukamin saja, wanda ya fito daga yankin Siberia na Rasha ya amsa cewa ya kashe fara hula mai shekaru 62, Oleksandr Shelipov a kauyen Chupakhivka dake arewa maso gabashin Ukraine.

ya yi ikirarin cewa ya bindige Shelipov  ne sakamakon matsin lamba daga wani soja, a yayin da suke kokarin tserewa zuwa Rasha a wata motar da suka sata, a ranar 28 ga watan Fabrairu.

Shishimarin ya nemi afuwar mai dakin Shelipov, inda ya ce bai yi niyyar kisa ba, tsoro ne ya mamaye shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.