Isa ga babban shafi

Za a shafe shekaru 15 zuwa 20 kafin Ukraine ta samu shiga EU - Faransa

Kasar Faransa ta ce zai dauki shekaru 15 zuwa 20 kafin Ukraine ta zama cikakkiyar mamba a cikin kungiyar kasashen Turai, sabanin yadda shugaba Volodymyr Zelensky ke bukata cikin gaggawa.

Ministan da ke kula da harkokin kasashen Turai na Faransa Clement Beaune.
Ministan da ke kula da harkokin kasashen Turai na Faransa Clement Beaune. AP - Virginia Mayo
Talla

Ministan da ke kula da harkokin kasashen Turai a Faransa wadda ke jagorancin kungiyar EU na watanni 6 a wannan karo, Clement Beaune ya ce ya dace su fadawa kansu gaskiyar lamarin cewar ba zai yiwu Ukraine ta zama mamba a cikin watanni 6 ko shekara guda ko kuma 2 ba.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Turai na jan kafa wajen gaggauta amincewa da Ukraine a matsayin wakiliya, yayin da shugaba Emmanuel Macron ya ce za’a tattauna bukatar kasar a taron EU da zai gudana a watan gobe.

Kasar Faransa na daga cikin manyan kasashen yammacin Turai da ke baiwa Ukraine tallafin makamai da sauran kayayyakin aikin soji, domin taimaka mata wajen kare kanta daga mamayar sojojin Rasha, wadanda suka kaddamar da yaki kan makwafciyar ta su tun a ranar 24 ga watan Fabarairu na 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.