Isa ga babban shafi

'Yan kasar Spain sun yi zanga-zangar adawa da dawowar tsohon sarkinsu gida

Daruruwan mutane ne suka shiga zanga zangar adawa da komawar tsohon Sarkin Spain Juan Carlos gida, wanda ya koma kasar daga Daular Larabawa inda ya kwashe shekaru 2 yana gudun hiira.

Tsohon sarkin Spain, Juan Carlos, ya dawo ƙasarsa, a Sanxenxo, Galicia, 20 ga watan Mayu 2022.
Tsohon sarkin Spain, Juan Carlos, ya dawo ƙasarsa, a Sanxenxo, Galicia, 20 ga watan Mayu 2022. © AP - Lalo R. Villar
Talla

Kakakin gwamnatin Spain yace akalla mutane 300 suka gudanar da zanga zangar kusa da fadar Sarkin dake madrid domin nuna bacin ran su saboda zargin cin hanci da kuma halarta kudaden haramun da ake masa.

Wannan Litinin ake saran tsohon Sarkin ya ziyarci dan sa Sarki Felipe na 6 kafin komawa Daular Larabawa inda yake zama.

Gwamnatin Firaminista Pedro Sanchez na ci gaba da dakon bayanai akan dalilin da ya sa Juan Carlos ya sauka daga karaga a shekarar 2014 domin nada dan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.