An kawo karshen dutse mai awan wuta a Spain
Hukumomin Spain sun bayyana cewa, an kawo karshen ibtila’in dutse mai awan wuta da ya auku a tsibirin La Palma tare da lalata daruruwan gidajen jama’a da kuma tarin gonakai.
Wallafawa ranar:
Tsibirn na La Palma ya shafe tsawon watanni uku yana fama da wannan ibtila’in , amma kai tsaye ba a samu asarar rayuka ba ko kuma raunuka a sanadiyar wautar da dutsen ke amayarwa.
Alkaluma sun nuna cewa, akalla gidaje dubu 1 da 345 ne suka lalace a sanadiyar ibtila’in, da suka hada da makarantu da coci-coi da cibiyoyin kiwon lafiya da gonakai.
A karon farko kenan tun shekara ta 1971 da dutsen ke aman wuta a La Palma, yayin da kuma aka yi ta samun girgizar kasa a yayin ibtila’in.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu