Isa ga babban shafi
Rasha - uKRAINE

Ukraine ta zargi Rasha da kai hari makaranta mai dauke da mutane 90

Ukraine ta zargi Rasha da jefa bam a wata makaranta da ke yankin Luhansk inda mutane 90 ke samun mafaka, yayin da wani babban dan majalisar dokokin kasar Rasha shima ya zargi Amurka da taimawa sojojin Ukraine wajen tsara dabarunta na yaki, wanda ya ce hakan ya yi daidai da cewa Amurka ta tsunduma cikin yakin kai tsaye.

Wata makaranta a yankin Louhansk na kasar Ukraine da ake zargin Rasha da kai hari, 7/05/22
Wata makaranta a yankin Louhansk na kasar Ukraine da ake zargin Rasha da kai hari, 7/05/22 via REUTERS - STATE EMERGENCY SERVICES
Talla

Shugaban rundunar sojin yankin Luhansk Serhiy Hayday ya ce wani jirgin saman Rasha ya jefa bam a makarantar da ke kauyen Bilohorivka mai nisan mil 7 daga fagen daga.

Hayday ya ce kawo yanzu an ceto mutane 30 daga baraguzan ginin.

Ya ce ana ci gaba da aikin ceto, yayin da Hotunan da hukumomin yankin suka wallafa sun nuna yadda makarantar ta ruguje.

Wata makaranta a yankin Bilohorivka na kasar Ukraine da ake zargin Rasha da kai hari. 7/05/22
Wata makaranta a yankin Bilohorivka na kasar Ukraine da ake zargin Rasha da kai hari. 7/05/22 via REUTERS - STATE EMERGENCY SERVICES

Vyacheslav Volodin ya wallafa wannan zargi ta shafinsa  na Telegram hakan tamkar Washintan ta dauki matakin soji ne kan Rasha.

Zargin Rasha

Kasashen Amurka da turai da ke cikin kawancen NATO sun taimawa Ukraine da manyan makamai domin taimaka kare kanta daga hare-haren Rasha wanda ya kai ga mamaye wasu sassan gabashi da kudancin Ukraine amma ta kasa kwace birnin Kyiv.

Sai dai Amurka da kawayenta na kungiyar tsaro ta NATO sun sha nanata cewa ba za su shiga yakin da kansu ba, domin gudun kada su shiga cikin rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.