Isa ga babban shafi
Iran-Faransa

Faransa na son a gaggauta kammala tattaunawar ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran

Kasar Faransa ta ce yana da matukar muhimmanci a kammala tattaunawar da wakilan kasashen duniya ke yi wajen cimma matsaya kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a wannan mako.

Zaman tattaunawar kokarin ceto yarjejeniyar Nukiliyar Iran a Vienna.
Zaman tattaunawar kokarin ceto yarjejeniyar Nukiliyar Iran a Vienna. © via REUTERS - EU Delegation in Vienna
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana wannan matsayi sakamakon ci gaban da kowanne bangare yayi shelar samu.

Kasashen dake cikin yarjejeniyar ta shekarar 2015 na kallon wannan yunkuri a matsayin hanyar da ta rage na hana kasar Iran gina makamin nukiliya zargin da kasar ke ci gaba da musantawa.

Yanzu haka babban jami’in dake wakiltar Iran wajen tattaunawar Ali Bagheri ya koma Vienna daga Tehran inda yaje tuntuba domin ci gaba da shiga taron.

Kasashen dake cikin tattaunawar sun hada da Faransa da Jamus da Birtaniya da Rasha da China da kuma Amurka bayan ita Iran.

Yarjejeniyar ta shekarar 2015 ta ragewa Iran takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba mata saboda shirin nukiliyar, amma sai kasar Amurka tayi gaban kan ta wajen janyewa daga cikin ta a shekarar 2018 lokacin jagorancin shugaba Donald Trump wanda ya sake sanyawa Iran sabbin takunkumin karya tattalin arziki.

Wannan mataki na Trump ya sa Iran ta koma ci gaba da shirin tace sinadarin uranium da ake zargin zata gina makamin da shi.

Yayin gudanar da wannan taro na Vienna Iran tayi ta bukatar bata tabbacin cewar gwamnatin Joe Biden ba zata dauki irin matakin da Donald Trump da ya gada ta dauka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.