Isa ga babban shafi
Turai - Guguwa

Guguwar Eunice ta kashe mutane 9 a sassan Turai

Guguwar Eunice ta kashe akalla mutane tara a Turai, kamar yadda wasu alkalumma suka nuna a ranar Juma'ar nan.

Yadda guguwar Eunice ta afkawa wasu sassan kudancin Birtaniya.
Yadda guguwar Eunice ta afkawa wasu sassan kudancin Birtaniya. Geoff Caddick AFP
Talla

Guguwar dai ta fara ne da hargitsa wasu yankunan Birtaniya, inda ta tilastawa miliyoyin mutane neman mafaka yayin da ta katse sufurin jiragen sama da na kasa, da kuma na ruwa a sassan yammacin Turai.

A birnin London 'yan sanda sun ce wata mata 'yar shekara 30 ta mutu bayan da wata bishiya ta fada kan wata mota da take fasinja a ciki. Shi kuma wani mutum a arewa maso yammacin Ingila ya rasa ransa ne bayan da tarkacen gine-gine ya afkawa gilasan motar da yake tafiya a ciki.

A Netherlands mutane 3 suka mutu sakamakon fada musu da bishiya ta yi, sai kuma wani mutum a gabashin Ireland, yayin da wani dan kasar Canada mai shekaru 79 ya mutu a Belgium.

Wani direban mota kuwa ya mutu ne a lokacin da motarsu ta yi karo da wata bishiya da ta fada kan wata hanya kusa da Adorp a lardin Groningen da ke arewacin Netherlands.

A Jamus kuma, wani direban mota ya mutu bayan da wata bishiya ta buge motarsa ​​a kusa da garin Altenberge.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.