Isa ga babban shafi

Christiane Taubira ta fi farin jinin tsayawa takarar zaben Faransa

Zaben fidda gwanin da jama’a suka gudanar a kasar Faransa ya baiwa tsohuwar ministar shari’ar kasar Christiane Taubira damar zama sahun gaba cikin wadanda suka fi farin jinin tsayawa takarar zaben shugaban kasar da za’ayi a wannan shekarar.

Christiane Taubira, Tsohuwar Ministar shara'ar Faransa
Christiane Taubira, Tsohuwar Ministar shara'ar Faransa AFP - THOMAS COEX
Talla

Magoya bayan Jam’iyyar Socialists 467,000 suka yi rajistar kada kuri’a a zaben fidda gwanin ta intanet wanda aka gudanar tsakanin ranakun alhamis zuwa jiya lahadi, wanda ya kimanta yan takarar shugaban guda 7 da suka hada da Yan siyasa 5 da Yan kungiyar fararen hula guda 2.

Christiane Taubira yar takara a zaben shugabancin Faransa
Christiane Taubira yar takara a zaben shugabancin Faransa AP - Kamil Zihnioglu

Taubira wadda ta shiga takarar a matsayin wadda tafi farin jinni ta zama wadda ke sahun gaba a kuri’un da aka kada, sai kuma Yannick Jadot na Jam’iyyar Green sannan mai tsatsauran ra’ayi Jean-Luc Melenchon da Dan Majalisar Turai Pierre Larrouturou da kuma Anne Hidalgo, mai rike da mukamin Magajin Garin Birnin Paris.

Anne Hidalgo,Magajin birnin Paris
Anne Hidalgo,Magajin birnin Paris THOMAS LO PRESTI AFP

Sai dai zaben ya gamu da suka daga wasu daga cikin Yan takarar da suka hada da Melenchon da Jadot da kuma Hidalgo.Kuri’ar jin ra’ayin jama’a sun bayyana cewar babu wani daga cikin wadannan Yan takarar da zai wuce zagaye na farko na zaben gama gari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.