Isa ga babban shafi
Amurka - Guguwa

Guguwa ta kashe mutane sama da 70 a kasar Amurka

Wata mahaukaciyar guguwa ta halaka mutane sama da 70 bayan da ta afkawa Kentucky da ke kudu maso gabashin Amurka, kamar yadda gwamnan jihar Andy Beshear ya shaida wa manema labarai.

Kadan daga cikin yadda kakkarfar guguwa ta ltayi barna a jihar Kentucky da ke kasar Amurka.
Kadan daga cikin yadda kakkarfar guguwa ta ltayi barna a jihar Kentucky da ke kasar Amurka. © ABC13
Talla

Gwamnan ya kuma bayyana fargaba kan yiwuwar adadin mamatan ya zarce  100 la’akari da cewar kakkarfar guguwar ce mafi hatsari a tarihi da ta afkawa jihar tasa.

Guguwar dai ta lalata larduna da dama a jihar ta Kentucky, yayin da take tsala gudun kilomita kusan 240 a sa’a 1.

Tuni dai guguwar ta yi barna a wasu sassan jihohin Amurka baya ga Kentucky, inda a ranar Juma’a ta yi kaca kaca da wani babban shagon sayar da kayayyaki na Amazon da ke jihar Illinois, yayin da kafafen yada labarai na cikin gida suka ba da rahoton cewa akwai kusan ma'aikata 100 makale a cikin sauran ginin katafaren shagon.

Jami'ai dai na cigaba da aikin ceto wadanda guguwar ta rutsa da su.

A jihar Tennessee kuwa, akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon guguwar da ta afku, kamar yadda wani jami’in bayar da agajin gaggawa ya shaidawa kafafen yada labaran cikin gidan Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana guguwar a matsayin gagarumar iftila'in da ta afakawa kudancin da arewa maso yammacin kasar.

Biden yace rasa 'dan uwa a irin wannan iftila'i abin tashin hankali ne, yayin da yace suna aiki tare da gwamnonin yankin domin taimaka musu da abinda suke bukata wajen aikin jinkai da gano wadanda suka tsira da kuma kiyasin asarar da akayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.