Isa ga babban shafi
Faransa - Birtaniya

Faransa ta ce ba za ta yi watsi da masuntar ta ba a rikicinta da Birtaniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya dage cewa ba zai "yi watsi da bukatun" masuntar kasar da ke neman lasisin kamun kifi a tsibirin Channel na Jersey, kamar yadda yarjejeniyar bayan Brexit ta tanadar, lamarin da ke haifar da munanan kalamai tsakanin kasashen biyu dake neman rikidewa zuwa yakin kasuwanci.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron addressing yayin taron tsaro da wasu shugabannin kasashen duniya
Shugaban Faransa Emmanuel Macron addressing yayin taron tsaro da wasu shugabannin kasashen duniya © Nigeria presidency
Talla

Yayin wata ziyara da ya kai arewacin kasar ranar Jumma’a shugaba Macron yace za su ci gaba da fafutuka, ba tare da yin kasa a guiwa ba kan bukutun masuntan kasar.

Macron ya yi kira ga Hukumar Tarayyar Turai da ta kara zage damtse wajen tursasawa Jersey, dake karkashin Birtaniyya, don girmama sharuddan yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar bayan ficewar Birtaniya daga cikin gungun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.