Isa ga babban shafi
Faransa- birtniya

Rikicin kamun kifi na kara ta'azzara tsakanin Birtaniya da Turai

Birtaniyya ta yi gargadin cewa za ta fara aiwatar da sabbin bincike kan jiragen ruwan kamun kifi na Tarayyar Turai idan Faransa ta aiwatar da barazanarta na daukar matakan ramuwar gayya a takaddamar da ta biyo bayan dokokin ruwan bayan Brexit.

Matsunta Faransa a tekun Boulogne-sur-Mer, dake Kudancin kasar, 28/12/2020
Matsunta Faransa a tekun Boulogne-sur-Mer, dake Kudancin kasar, 28/12/2020 REUTERS - CHARLES PLATIAU
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, matsayin Birtaniyya na kan layi  a takaddamar, yana mai zargin London da yin watsi da yarjejeniyar Brexit da aka amince da ita bayan shafe shekaru ana tattaunawa.

To saidai Firaynministan Burtaniya Boris Johnson, wanda zai yi gajeriyar tattaunawa ta gaba da gaba da Macron a taron G20 da za’a bude yau a birnin Rome na kasar Italiya, ya sha alwashin kare muradun Burtaniya.

Faransa ta fusata cewa Biritaniya da tsibiran Jersey da Guernsey masu cin gashin kansu, wadanda suka dogara da London don tsaro da harkokin waje, sun ki baiwa jiragen ruwan Faransa lasisin kamun kifi a cikin ruwansu bayan Brexit.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.