An fara bincike kan zargin fyade a fadar Macron
Masu gabatar da kara a Faransa na ci gaba da bincike kan zargin da ake yiwa wani soja da yiwa abokiyar aikin sa Fyade a fadar shugaban kasar, abinda ake ganin ka iya shafawa gwamnatin shugaba Macron kashin kaji.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan da shugaban Kasar Emmanuel Macron ya bar wajen taron karrama manyan sojojin kasar tun a watan Yulin da ya gabata.
Sojojin biyu dai na cikin wadanda aka tura don tabbatar da tsaro a fadar shugaban kasar a ranar, a lokacin ne kuma sojan ya hilaci abokiyar aikin sa tare da yi mata Fyaden.
Sojan da ake zargi dai ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata, sai dai kuma an bukaci da ya rika ci gaba da amsa tambayoyin jami’an tsaro duk da cewa a baya ba’a gurfanar da shi gaban kotu a hukumance ba.
Fadar shugaban Faransa dai na kokari wajen ganin cewa abin kunya bai fita ta bangaren gwamnati ba, amma da alama hakan bata yiwuwa don kuwa ko a baya-bayan nan ma kotu ta yankewa wani dogarin Shugaba Macron Hukuncin daurin shekaru 3 sakamakon naushin wani cikin masu zanga-zanga a watan Mayun 2018.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu