Isa ga babban shafi
Faransa

An tsinci gawar wata tsohowa mai shekaru 77 da aka fillewa kai a gidanta

Hukumomin Faransa sun gano gawar wata mata mai shekaru 77 da aka fillewa kai a gidanta da ke wani wurin shakatawa da ke kudancin kasar.

'Yan sandan Faransa dake sintiri a birnin Paris, 29/04/21.
'Yan sandan Faransa dake sintiri a birnin Paris, 29/04/21. REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Wata majiyar 'yan sanda, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a halin yanzu hukumomi ba sa kallon lamarin da ta'addanci saboda ba musu gabatar da karar kan ayyukan ta’addanci bane ke bincike.

Majiyar ‘yan sandan tace an gano gawar matar a gidanta dake Agde da ke yankin Herault a gabar tekun Mediterranea a kudancin Faransa.

'Yan sanda sun ziyarci gidan tsohuwar ce bayan da danta ya sanar da su rashin jin duriyarta, sakamakon yadda suka saba waya kullum, sannan kuma ya leka gidan ta hoton bidiyo kuma ya kalli wani abu kamar inuwa a ƙasa.

Wata majiyar kuma tace, kan matar na kan tebur kusa da gawar, kuma babu wani alamun balle kofar shiga dakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.