Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta karrama wadanda suka mutu a hare-haren 9/11 shekaru 20 da suka wuce

Shekaru 20 bayan harin 11 ga watan Satumba a kan  ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da  hasumiyar Hukumar Kasuwanci ta duniya, al’ummar Amurka sun taru don karrama kusan mutane dubu 3000 da harin na 11 ga watan Satumban 2001 ya lakume rayukansu.

Iyalan wadanda suka mutu a hare haren 9/11 dauke da hotunansu a wajen bikin tunawa da su birnin New York na Amurka, 11 ga Satumba, 2021.
Iyalan wadanda suka mutu a hare haren 9/11 dauke da hotunansu a wajen bikin tunawa da su birnin New York na Amurka, 11 ga Satumba, 2021. REUTERS - POOL
Talla

Bikin na ranar Asabar da aka gudanar a dandalin da aka kebe don tunawa da wadanda harin ya rutsa da su a birnin New York, an fara shi ne da yin shuru na dan lokaci karfe 8 da minti 46 na safe, daidai da karfe 12 da minti 46 na rana agogon GMT, daidai lokacin da jirgin farko da aka karkata akalarsa ya daki tagwayen hasumiyar hukumar kasuwanci ta duniya.

Daga nan ne ‘yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su suka fara karanta sunayen  mutane dubu 2 da 977 tsawon sa’o’i 4, cikin hawaye da shasshekar kuka.

Masu jimami na dauke da hotunan makusantansu da suka mutu, a yayin da shahararren mawaki, Bruce Springsteen yake rera wakarsa mai taken ‘Ill See you in My Dreams.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai tsohon shugaban Amurka George W. Bush, wanda a zamanin mulkinsa aka kai wannan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.