Isa ga babban shafi
New Zealand

An harbe maharin da ya jikkata mutane 6 a New Zealand

Wani mahari da ke ikirarin biyayya ga kungiyar IS ya jikkata akalla mutane 6 ta hanyar daba musu wuka a wani babban kanti da ke New Zealand a yau Juma'a kafin daga bisani 'yan sandan da ke bibiyar mutumin su harbe shi har lahira.

Jami'an 'yan sandan New Zealand a wajen wani kantin sayar da kayayyaki bayan harin da wani mutum ya kaiwa mutane da wuka a garin Auckland. 3 ga Agusta, 2021.
Jami'an 'yan sandan New Zealand a wajen wani kantin sayar da kayayyaki bayan harin da wani mutum ya kaiwa mutane da wuka a garin Auckland. 3 ga Agusta, 2021. via REUTERS - REUTERS TV
Talla

Fira Ministan New Zealand Jacinda Ardern ta ce mutumin, dan asalin Sri Lankan da ya shiga a shekarar 2011, wanda kuma ke cikin jerin mutanen da aka sa wa ido bisa zargin alakarsu da ta'addanci, ya shiga wani kantin sayar da kayayyaki a cikin garin Auckland ne, inda ya duki wuka daga cikin wadanda aka jera domin saidawa, nan take kuma ya afkawa jama’a.

Fira Ministan kasar New Zealand Nova Jacinda Ardern.
Fira Ministan kasar New Zealand Nova Jacinda Ardern. AP - Robert Kitchin

Arden ta ce daga cikin mutane shida da maharin ya jikkata, uku sun samu munanan raunuka.

Fira Ministan ta bayyana harin a matsayin abin kyamar da ba ya wakilcin wani addini ko wata al'umma.

Harin ta'addanci mafi muni da kasar New Zealand ta gani dai shi ne wanda wani dan bindiga ya kashe Musulmai 51 tare da jikkata wasu akalla 40 yayin da suke ibada a masallatan birnin Christchurch a cikin watan Maris na shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.