Isa ga babban shafi
New Zealand

Jami’an tsaro sun gaza wajen dakile harin ta’addanci kan Masallatai - Rahoto

Wani Rahoton bincike a New Zealand ya nuna gazawar jami’an tsaro wajen sanya ido kan mutumin da ya kai hari Masallatai bara ya kuma kashe mutane 51 a Christchurch.

Wasu 'Yan sandan kasar New Zealand
Wasu 'Yan sandan kasar New Zealand TVNZ via REUTERS TV
Talla

Rahoton binciken ya bukaci gagarumin sauyi kan yadda ake gudanar da aikin yaki da ta’addanci sakamakon kazamin harin da yayi sanadiyar kashe Musulmi masu ibada 51.

Rahoton mai shafi 800 yace jami’an leken asiri sun mayar da hankali kan sosai kan masu tsatsauran ra’ayin Islama, ba tare da mayar da hankali sosai kan fararen fata masu tsatsauran ra’ayi ba.

Fira Minista Jacinda Arden ta yaba da rahoton inda ta sha alwashin duba shawarwari 44 dake ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.