Isa ga babban shafi
Turkiya

Hatsarin mota ya hallaka muatane 12 tare da jikkata 26 a Turkiya

Hukumomin Turkiya sukace, Mutane 12 ne suka mutu wasu 26 kuma suka jikkata lokacin da wata motar bas dauke da bakin haure ta yi hadari a gabashin kasar cikin daren Asabar.

Hadarin mota a wani yanki na Turai ranar 2 ga watan Satumbar 2012.
Hadarin mota a wani yanki na Turai ranar 2 ga watan Satumbar 2012. REUTERS/Philippe Laurenson
Talla

Daga cikin wadanda suka mutu har da bakin haure 11 da kuma wani mutum da ya taimaka wajen shirya safarar tasu ba bisa ka’ida ba.

Yanzu haka wadanda suka jikkata na karban magani  a wani asibiti dake yankin Van, yayin da jami’an tsaro suka tsare mai motar bas din.

Garin Van wanda yake kusa da kan iyakar gabashin Turkiya da Iran, ana amfani da shi wajen tsallakawa da bakin haure ta doguwar tafiya zuwa Turai, hanyar da akasari ‘yan Afghanistan ke bi.

A watan Yulin shekarar 2020, wani jirgin ruwa dauke da bakin haure 60 ya nitse a tafkin Van.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.