Isa ga babban shafi
EU-Rasha

EU ta yi watsi da bukatar Jamus da Faransa kan tattaunawa da Rasha

Taron shugabannin Turai ya yi watsi da shawarar da shugaban Faransa Emmanel Macron da takwararsa ta gwamnatin Jamus Angella Merkel suka gabatar, da ke nenam bude tattauwa da shugaba Vladimir Putin na Rasha don rage zaman tankiya a tsakanisnu.

Wata ganawar Vladimir Putin na Rasha da takwarorinsa na Jamus da Faransa, Angela Merkel da Emmanuel Macron.
Wata ganawar Vladimir Putin na Rasha da takwarorinsa na Jamus da Faransa, Angela Merkel da Emmanuel Macron. AFP - CHARLES PLATIAU
Talla

Shugaban kasar Lithuania Gitanas Nausetda, ya ce shugabannin gungun na Turai, sun yi watsi da wannan shawara ce bisa dalilan cewa ba wani sauyin da suka gani a zahiri da zai sa su shirya ganawa kai-tsaye da shugaba Putin a hanlin yanzu.

Kasar Rasha bisa jagorancin Vladimir Putin na fuskantar takun saka da zaman tankiya tsakaninta da gungun kasashen na EU baya ga dai daikun kasashen yammacin Duniya ta kusan kowacce fuska kama daga Diflomasiyya da cinikayya, tattalin arziki da kuma uwa uba dokokin kare hakkin dan adam.

Sai dai taron shugabannin na Turai ya amince ci gaban tattaunawa da Turkiyya domin rage zaman tankiyar da ake yi tsakanin kasar da kuma kasashen Girka da Cyprus.

Yanzu haka dai Tarayyar Turai na nazarin bai wa Turkiyya Euro bilyan 4 don hana ‘yan gundun hijirar Syria milyan 3 da rabi tsallakawa zuwa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.