Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Putin ya sanar da shirin ganawa da Zelensky na Ukraine a Kremlin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana shirinsa na tarbar takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky a fadarsa ta Kremlin,  amma ya kafa masa sharadin zama tare da ‘yan aware domin tattaunawa da su kan rikicin yankin Crimea.

Shugaban Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Rasha Vladimir Putin. AP - Alexei Druzhinin
Talla

A yayin  ganawa da shugaban Belarus, Alexander Lukshenko, shugaba Putin ya ce, Zelensky na iya kawo masa ziyara a birnin Moscow kowanne lokaci daga yanzu.

Gayyatar na zuwa ne bayan Zelensky ya bukaci zama tare da Putin a yankin gabashin Ukraine, inda ake fargabar tsanantar rikici tsakanin sojojin Ukraine da ‘yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha.

Sai dai Putin ya hakikance cewa, sai dai su hadu a birnin Moscow.

A bangare guda, tuni Rasha ta fara janye  dubban dakarunta da ta girke a kusa da kan iyakar Ukraine  daga yau juma'a, dakarun da a baya ta girke don gudanar da atisayen soji dauke da manyan makamai, lamarin da ya dada dagula dangantakarta da kasashen yammacin Duniya.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ce, a wannan Juma’ar ake fara janye dakarun domin komawa sansaninsu na din-din-din bayan cimma muradun girke su.

Tuni kungiyar tsaro ta NATO ta ce, tana bibiyar sanarwar Rasha ta janye dakarun nata, tana mai cewa, duk wani matakin sassauta tankiya na da muhimmanci kuma tun da jimawa ya kamata a yi haka a cewarta.

NATO ta jaddada kira ga Rasha da ta mutunta dokokin kasa da kasa , sannan ta janye daukacin sojojinta daga Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.