Isa ga babban shafi
Turai-Rasha

Putin ya gargadi kasashe kan yiwa Rasha shisshiga a harkokin cikin gida

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gargadi kasashen yammacin duniya da su kiyayi wuce gona da iri kan harkokin cikin gidan kasar sa, a dai dai lokacin da ake takun saka tsakanin sa da su kan tsare shugaban 'yan adawa Alexie Navalny.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. REUTERS - EVGENIA NOVOZHENINA
Talla

Yayin da ya ke gabatar da jawabin sa na halin da kasa ke ciki a gaban 'yan Majalisu, shugaba Putin ya ce Rasha za ta mayar da martani cikin gaggawa kuma mai tsauri kan duk wanda ya taka muradunta, yayin da ya yi Allah wadai da abinda ya kira yunkurin juyin mulki a Belarus.

Putin ya ce duk masu takalar manufofi da muradun Rasha za su yi nadamar haka, fiye da wata nadamar da suka taba yi na dogon lokaci.

Shugaban ya yaba rawar da Rasha ke takawa wajen yaki da cutar korona da kuma samar da maganin rigakafi, yayin da ya sanar da shirin kashe kudade a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben 'yan majalisu a cikin wannan shekarar.

A dai dai lokacin da shugaba Putin ke jawabin masu zanga zangar adawa da tsare Alexie Navalny sun fara gangami a sassan kasar, yayin da shugaban yaki furta komai game da halin da ya ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.