Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

Birtaniya da EU sun kammala sa hannu kan yarjejeniyar Brexit

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai EU sun kammala sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci tsakaninsu da Birtaniya da yammacin ranar Laraba, inda tawaga ta musamman ta dauki kunshin yarjejeniyar don kai ta London, dai dai lokacin da ya rage sa’o’i kalilan kasar ta kammala ficewa daga kungiyar, bayan shafe kusan shekaru 100 a kungiyar.

Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson tare da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson tare da shugabar hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Daniel LEAL-OLIVAS / AFP
Talla

Yarjejeniyar mai shafi dubu 1 da 246 da ke dauke da sa hannun Ursula von der Leyen da Charles Michel shugaban kungiyar da kuma shugabar majalisar EU, sun ce lokaci ya yi da za su ajiya batun Brexit a gefe.

Tun a yammacin ranar ta Laraba, tawaga ta musamman ta dauki kunshin yarjejeniyar tare da mikata ga Firaminista Boris Johnson wanda zai gabatarwa Majalisa ita tare da tafka muhawarar karshe gabanin wayewar garin gobe Juma’a.

Jawabin da ya gabatar ga Downing Street Johnson ya ce yarjejeniyar ita ce jituwa mafi daraja da bangarorin biyu suka cimma don dorewar zaman tare da kuma fahimtar juna.

Yayin da ya ke jawabi ga majalisar gabanin fara tafka muhawara kan yarjejeniyar, Firaministan na Birtaniya ya ce bisa tanade-tanaden da ke kunshi a yarjejeniyar kasuwancin da Birtaniya ta kulla da EU, ko shakka babu bangarorin biyu za su ci gaba da zamowa manyan abokai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.