Isa ga babban shafi
Birtaniya-EU

Brexit: EU ta sallama kashi 25 na yankin ruwan da take kamun kifi

Bayan shafe watanni 11 ana kwan gaba kwan baya a tattaunawar da wakilan Birtaniya da na kungiyar tarayyar Turai ke yi kan yarjejeniyar Brexit, ranar Alhamis 24 ga watan Disamba suka kulla yarjejeniyar kasuwancin da za su yi aiki da ita bayan cikar wa’adin rabuwarsu ta dindindin a ranar 31 ga watan.

Wani mutum dauke da tutocin Birtaniya da na kungiyar tarayyar Turai
Wani mutum dauke da tutocin Birtaniya da na kungiyar tarayyar Turai Henry Nicholls/Reuters
Talla

Bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyar ce bayan cimma matsaya kan baatutuwan da suka shafi hakkokin sauran kasashe 27 na kungiyar EU na gudanar da sana’ar Su a ruwa ko yankin tekun dake Birtaniya.

Kafin cimma yarjejeniyar dai sai da kasashen kungiyar EU 27 suka sallama kashi 25 na yankin ruwan da suke sana’ar Su ga Birtaniya domin kaucewa cikar wa’adin rabuwarsu da dindindin kafin karshen watan nan.

Tuni dai shugabannin kasashen Turai suka aiki da sakwannin yabawa da karkare yarjejeniyar ta Brexit, wadda fira ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana a matsayin nasara ga dukkan Turai, yayinda shugaban faransa Emmanuel Macron yace kwalliya ta biya kudin sabulu dangane hadin kan da kasashen Turai suka yi kafin cimma yarjejeniyar.

Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bayyana fatan ganin sakamako mai kyau tayi daga yarjejeniya da suka kulla da Birtaniya, yayinda ministan harkokin wajen Denmark Jeppe Kofod ya kira yarjejeniyar da kyautar Kirsimeti.

Ranar 30 ga watan nan na Disamba majalisar Birtaniya za ta nazarci yarjejeniyar ta Brexit.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.