Isa ga babban shafi

Ana halin rashin tabbas kan yarjejeniyar ciniki tsakanin Birtaniya da Turai

Batun cimma yarjejeniyar kasuwancin bayan rabbuwa tsakanin Birtaniya da Tarayyar Turai na cikin halin tabbas a wannan Asabar, bayan bayanai masu kashe gwiwa daga shugabannin bangarorin biyu, a yayin da ya rage ‘yan sa’o’i a karkare tattaunawar karshe.

Boris Johnson da Ursula von der Leyen.
Boris Johnson da Ursula von der Leyen. Daniel LEAL-OLIVAS / AFP
Talla

Fira minista Boris Johnson da shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen sun bai wa masu tattaunawar zuwa wannan Lahadi su yanke shawarar ko za su ci gaba da tattaunawar ko kuma su hakura da ita.

Al’amarin ya rincabe bayan daa shugabar hukumar Tarayyar Turai, von der Leyen shaida wa jagororin Turai a birnin Brussels cewa ba a sa rai ga komai, kuma akwai yiwuwar karkare tattaunawar babu yarjejeniya.

Ireland da Jamus sun yi kokarin karfafa gwiwa, inda suke cewa duk da sarkakiyar da ke akwai, ana iya cimma yarjejeniya.

Amma fira minista Johnson ya fito yana cewa alamu sun nuna ana iya tashi baram baram, babu yarjejeniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.