Isa ga babban shafi
Faransa

Masu zanga-zanga sun jikkata 'yan sanda 67 a Faransa

‘Yan sandan Faransa akalla 67 ne suka jikkata yayin arrangama da masu zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tsaro da gwamnatin kasar ta gabatar.

Masu zanga-zanga yayin arrangama da 'yan sanda a birnin Paris.
Masu zanga-zanga yayin arrangama da 'yan sanda a birnin Paris. France24
Talla

Yayin karin bayani ministan cikin gidan Faransar Gerald Darmanin ya ce 48 daga cikin ‘yan sandan 67 an jikkata su ne a birnin Paris, yayin zanga-zangar da sama da mutane dubu 50 suka fita.

Kawo yanzu jami’an tsaron Faransar sun damke mutane 95 daga cikin gungun masu boren da suka yi arrangama da su.

Karkashin sabuwar dokar tsaron dai gwamnatin Faransar ta haramta daukar hotunan ‘yan sanda yayin gudanar da ayyukansu, abinda ‘yan adawa da sauran kungiyoyin fararen hula suka bayyana da take hakkin ‘yancin fadin albarkacin baki musamman ga manema labarai, abinda zai baiwa jami’an tsaron damar cin karensu ba babbaka yayin cin zarafin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.