Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan Sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Faransa

'Yan Sanda a Paris da ke kasar Faransa sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa dubban masu zanga-zanga da suka mamaye titunnan birnin suna fashe-fashe da kone-kone a dai dai lokacin da ake gudanar da ranar ma’aikata ta duniya a ranar Laraba.

Jami'an 'Yan Sandan Faransa sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Paris
Jami'an 'Yan Sandan Faransa sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Paris REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Tun kafin bikin ranar ma’aikatan, gwamnatin Faransa ta girke jami’an tsaro 7,400 a birnin Paris kadai, saboda abinda ta kira bayanan asirin da ta samu na yunkurin tayar da hankali da masu shirya zanga-zangar adawa da gwamnati ke yi a wannan ranar.

Wannan yasa shugaba Emmanuel Macron ya umurci jami’an tsaro da su yi amfani da karfi muddin aka kalubalance su.

An dai fara samun tashin hankali ne lokacin da masu zanga-zangar da masu bikin ranar ma’aikata suka yi gangami a Montpanesse, in da wasu mutane daga cikin taron sanye da bakin kyalle suka kutsa kai domin karbe ragamar gangamin, kuma suka fara jifar jami’an tsaro da duwatsu da kuma kwalabe, abinda ya sa suka harba musu barkonon tsohuwa.

Ma’aikatar Cikin Gidan kasar ta ce, masu zanga-zangar 24 sun samu raunuka, yayinda aka kama 380.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.