Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta girke jami'an tsaro don gudun rikici a bikin ranar ma'aikata

Hukumomin kasar Faransa sun ce za su girke jami’an 'yan Sanda 7,400 a birnin Paris domin fuskantar duk wani kalubale da ke iya tasowa sakamakon bikin ranar ma’aikatan da zai gudana a yau.

Wasu jami'an 'yan sanda a birnin Paris na Faransa
Wasu jami'an 'yan sanda a birnin Paris na Faransa Reuters
Talla

Gwamnatin kasar ta ce akwai alamun cewar bikin na yau zai zama mai matukar tsauri, ganin yadda masu adawa da manufofin shugaba Emmanuel Macron da ke gudanar da zanga zanga, suka yi watsi da tayin zaftare harajin da shugaban ya gabatar musu.

Ministan cikin gida Christophe Castaner ya ce sun gano yadda kungiyoyi ke kiran jama’a ta kafar sada zumunta domin tayar da hankali a birnin.

Mai Magana da yawun gwamnati, Sibeth Ndiaye, ta ce shugaba Macron ya bai wa jami’an tsaron umarnin daukar mataki mai tsauri muddin suka fuskanci kalubale daga masu zanga zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.