Isa ga babban shafi

Trump zai janye dakarun Amurka daga Somalia

Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin janye dakarun Amurka da ke aikin kakkabe ‘yan kungiyar Al-Shabaab a Somalia, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana.

Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump MANDEL NGAN / AFP
Talla

Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron ta Pentagon ta ce ba Amurka na janyewa kacokan daga Afrika bane, a daidai lokacin da ake nuna damuwa a game da janyewarta a sassa dabam dabam na nahiyar, tana mai cewa za ta ci gaba da sa kafar wando daya da masu tsatsaurar ra’ayin addini.

Amurka tana da dakaru akalla 700 daga hukumomin tsaronta da ‘yan kwangila masu zaman kansu a Somalia, wandanda ke kaddamar da hare hare a kan kungiyar Al- Shabaab, tare da samar da horo ga sojojin Somalia.

Amurka ta yi asarar wasu daga cikin dakarunta a yankin, ciki har da wani jami’in hukumar leken asiri ta CIA a karshen watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.