Isa ga babban shafi
Amurka

Jihohin Amurka da ka iya sauya alkaluman zaben shugabancin kasar

Yayin da Amurkawa ke jiran sakamakon kidayar kuri’unsu a zaben shugabancin kasar da ake fafatawa tsakanin shugaba mai ci Donald Trump da abokin hamayyarsa Joe Biden, hankulan kwararru ko masu sharhi kan siyasar Amurka na kan wasu jihohi 5 da ke iya sauya alkaluman zaben kasar.

Taswirar wasu jihohin Amurka da ka iya sauya alkaluman zaben shugabancin kasar
Taswirar wasu jihohin Amurka da ka iya sauya alkaluman zaben shugabancin kasar National Popular Vote
Talla

Jihohin da suka hada da Pennsylvania, Michigan, Wisconsin, Georgia da kuma Florida na da muhimmanci ne la’akari da yawan masu kuda kuri’ar da suka kunsa da kuma wakilan musamman na kwamitin zaben shugaban kasa dake yanke hukuncin karshe sakamakon zaben shugabancin Amurkan.

A karkashin tsarin zaben na Amurka dai, dan takara na bukatar samun rinjaye a tsakanin wakilan kwamitin zaben shugaban kasar ko da kuwa shi/ita ke kan gaba wajen samun kuri’un jama’a gama gari, wanda akasin haka ke hana tabbatuwar nasarar dan takarar.

Jam’iyyar adawa ta Democrats dai na fatan kar ta sake samun matsalar da ta fuskanta a zaben shekarar 2016, lokacin da kuri’u daga jihohi 3 cikin biyar din suka sauya alkaluman nasarar data kama hanyar samu.

Shugaba Donald Trump ya lashe zaben 2016 ne bayan samun mafi rinjayen kuri’u da karamar tazara a Michigan, Wisconsin da kuma Pennsylvania, jihohin da jam’iyyar Democrats ke da kwarin giwar tace za ta lashe su.

Nasarar Trump a waccan lokacin ne kuma ta bashi damar samun rinjaye a kuri’un da wakilan musamman na kwamitin zaben shugaban kasa suka kada, duk da cewa ya sha kaye a hannun abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton, a kuri’un da sauran Amurkawa gama gari suka kada.

Pennsylvania

Mahaifar dan takarar jam’iyyar Democrats Pennsylvania ce mafi girma a tsakanin jihohi uku daga cikin biyar din da suka fi muhimmanci a zaben Amurka. Alkaluma sun nuna cewar Philadelphia da Pittsburgh birane mafi girma a jihar ta Pennsylvania jam’iyyar Democrats ke da rinjaye, sai dai a yankunan karkara jam’iyyar Republican ke kan gaba.

Michigan

Bincike ya nuna cewar masu kada kuri’a da dama a jihar Michigan da a baya ke marawa Republican baya sun komawa jam’iyyar Democrats, sai dai duk da haka a zaben shekarar 2016 shugaba Trump ya samu mafi rinjayen kuri’u.

Sai dai sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna cewar a wannan karon Joe Biden ke kan gaba wajen karbuwa a jihar da tazarar maki akalla 7 tsakaninsa da Trump.

Georgia

Tarihi ya nuna cewar babu wani dan takarar shugabancin Amurka daga jam’iyyar Democrats da ya taba lashe mafi rinjayen kuri’u a jihar Georgia tun bayan nasarar da Bill Clinton ya samu a shekarar 1992.

Sai dai bayanai sun ce yanzu haka karsashin jam’iyyar Republican mai mulki ya ragu matuka, bayanda wani dan majalisa daga jam’iyyar Democrats ya lashe mazabar jihar ta 6, yayin zaben gwajin tsakiyar zangon shugabancin Amurka da ya gudana a shekarar 2018. Kuri’ar jin ra’ayi ta nuna cewar Joe Biden na kan gaba wajen samun karbuwa a jihar ta Georgia da gajeriyar tazarar kusan maki 1, bisa shugaba mai ci Donald Trump.

Wisconsin

A shekarar 2016 Donald Trump ya kafa tarihin zama dan takarar jam’iyyar republican na farko da ya lashe mafi rinjayen kuri’u jihar Wisconsin, tun bayan nasarar tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan a shekarar 1984.

Trump ya samu nasarar ce bayan samun karbuwar da yayi a tsakanin ma’aikata farar fata da a baya ke marawa jam’iyyar Democrats baya.

Kawo yanzu bayanai sun nuna cewar Democrats ta fi rinjaye a biranen jihar ta Wisconsin ciki harda babban birnin jihar Madison da kuma Milwaukee, yayinda ita kuma jam’iyyar Republican tafi karfi a yankunan karkara.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ya nuna cewar Joe Biden ke gaban Donald Trump da maki 6 wajen samun karbuwa a jihar.

Florida

Yanzu haka Florida ce jiha ta uku mafi yawan al’umma a daukacin kasar Amurka wadda kuma ke da wakilan musamman na kwamitin zaben shugaban kasa guda 29.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a kafin ranar zabe ta nuna Biden ke kan gaba wajen samun karbuwa a jihar da kashi 48, yayin da Trump ke da kashi 43.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.