Isa ga babban shafi

Kakkarfar girgizar kasa ta hallaka sama da mutane 27 a Turkiya

Akalla mutane 12 suka mutu yayin da sama da 800 suka jikkata a yammacin Turkiya, bayan wata kakkarfar girgirzar kasa ta auku, wanda ta haddasa ragujewar Benaye, yayiin da ake ci gaba da aikin ceto.

Girgizar kasa a yankin Izmir na kasar Turkiya
Girgizar kasa a yankin Izmir na kasar Turkiya DHA via AP
Talla

Girgizar kasar da aka ji samatarta har a biranen Istanbul na Turkiyar da Athènes na kasar Girka ta auku ne a tekun Egée dake kudu maso yammacin Izmir, birni na 3 mafi girma a kasar Turkiya dake gab da tsibirin Samos na kasar Girka.

Tuni dai duk da sabanin siyasar da suke da shi kasashen na Turkiya da Girka suka bayyana aniyarsu ta yin aiki tare wajen taimakawa juna idan bukatar agaji ta taso.

Kasashen 2 sun dau wannan niyar ne bayan wata tattaunawa ta wayar Teleho da ta shiga tsakanin Ministocin harakokin wajen kasashen 2 ne kamar yadda wata sanarwa da ofishin harkokin wajen kasar ta Turkiya ta bayyana.

Sai dai anata bangaren Faransa ta bayyana aniyarta na son taimakawa da ayukan jinkai ga kasashen Turkiya da Girka a wannan lokaci da ake tsakkiyar takun saka da ta haifar da tsamin dangantaka tsakanin Farnsar da Turkiya kan yankin gabashin tekun Medtraniyan.

Franministan Girga Gremier Kyriakos Mitsotakis ya kirayi shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan inda ya gabatar masa da ta’aziyar mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon aukuwar girgizar kasar da ta shafi kasashen biyu makwabtan juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.