Isa ga babban shafi
Girka-Turkiya

Meditaraniya: "Ja da baya ga rago ba tsoro bane" inji Turkiya

Turkiya tace jirgin ruwan da ta aike don gudanar da bincike kan tarin iskar gas a gabashin tekun meditaraniya, ya koma gida a yau Lahadi.

Jirgin ruwan Turkiya da ya shafe wata guda yana bincike kan arzikin iskar gas a gabashin tekun Meditaraniya.
Jirgin ruwan Turkiya da ya shafe wata guda yana bincike kan arzikin iskar gas a gabashin tekun Meditaraniya. AFP
Talla

Sai dai ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar, yace janyewar tawagar binciken daga yankin da ake takaddama a kai, baya nufin sun hakura da hakkinsu.

Jirgin mai dauke da tawagar kwararru daga kasar ta Turkiya dai ya shafe akalla wata guda a gabashin tekun na Meditaraniya, abinda ya janyo zaman tankiya da yayi barazanar rikidewa zuwa ga daukar matakan soji, tsakanin kasar ta Turkiya da Girka, wadda sauran kasashen Turai ke marawa baya kan ikirarin yankin da ake takaddama a kai na cikin iyakarta.

A jiya Fira Ministan Girka Kyriakos Mitsotakis yace gwamnatinsa za ta sayi makamai masu yawan gaske gami da yiwa rundunar sojin kasar garambawul, a daidai lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin kasar ta Girka da Turkiya a gabashin Meditaraniya.

A karkashin shirin karfafa rundunar sojin nata mafi girma da aka gani a kusan shekaru 20, Girka ta cimma matakin sayen jiragen yaki 18 daga Faransa kirar Rafale, da jiragen yaki masu saukar ungulu na zamani guda 4, sai kuma daukar sabbin sojoji dubu 15, bayaga kara yawan makudan kudade a kasafin da take baiwa rundunar sojin nata, a bangaren kere-kere da kuma fasahar sadarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.