Rikicin kan iyaka bai hana Turkiya cigaba da neman gas a tekun Meditereniya ba
Kasar Turkiya ta cigaba da aikin neman iskar gas a cikin tekun Meditereniya da kuma bada umurnin cigaba da atisayen sojin ruwa, yayin da takaddama tsakanin ta da kasashen Girka da Faransa ke dada tsami saboda hako makamashin da kuma rikicin iyaka.
Wallafawa ranar:
A nata bangaren Girka ta sanar da kulla yarjejeniyar teku da kasar Masar, matakin da Turkiya ke adawa da shi saboda arzikin dake iyakokin kasashen biyu.
Ya zuwa jiya babu wata kasa tsakanin Turkiya da Girka dake nuna alamar sassautawa, yayin da kungiyar kasashen Turai ke kokarin ganin ta sanya bangarorin biyu sun hau teburin tattaunawa domin sasanta rikicin.
Tun a ranar laraba, 26 ga watan Agusta, Girka ta sanar da shirin kaddamar da atasayen soji na hadin gwiwa tare da Faransa, Italiya da Cyprus, a gabashin Meditereniya, yankin mai arzikin Iskar Gas da ake tankiya akai, tsakanin Turkiya, kasar ta Girka da kuma manyan kasashen Turan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu