Isa ga babban shafi

'Yan sandan Faransa sun hana yunkurin Checheniyawa na daukar fansa

Gwamantin Faransa ta bayyana cewa babu wata al'umma da za a yarda ta dauki doka a hannunta, bayan da 'yan sanda suka wargaza yunkurin checheniyawa na neman daukar fansa kan rikicikin kabilanci da ya jikkata dan uwansu.

'Yan sandan Faransa
'Yan sandan Faransa FRANCK FIFE / AFP
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Gerald Darmanin, ya bayyana hakan, bayan da ‘yan sanda suka tarwatsa gungun wata kabilar ‘yan kasar Checheniya mazauna kasar, tare da tsare mutane uku dauke da makamai da suka hada da wukake da adduna, da kuma sanduna.

Yanzu haka ana zargin Checheniyawan ‘yan asalin kasar Rasha mazauna garin Saint-Dizier da ke arewa maso gabashin Faransa, da neman kissa rikici, a yankurinsu na daukar Fansa kan dan uwansu mai shekaru 30 da ya jikkata bayan wani rikici tsakaninsu da Faransawa ranar Alhamis.

Ministan cikin gidan dake ziyarar a yankin Saint – Dizier, ya jinjiwa jami’an ‘yan sanda wajen dakatar da barkewar tarzoma, yana mai cewa baza su amincewa wata al’umma a fadin kasar daukar doka a hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.