Coronavirus: Kusan mutane 5500 sun mutu a Italiya
Kasar Italiya ta sanar da mutuwar mutane 651 ya ranar Lahadi, abin da ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa kusa da 5,500 daga cikin mutanen da suka kamu da cutar.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan adadi dai ya gaza na ranar Asabar inda aka samu 793, amma duk da haka shine na biyu mafi yawa a cikin wata guda.
Angelo Borrelli, jami’in hukumar kare jama’a ya bayyana fatar ganin adadin ya sauka cikin makwanni masu zuwa.
Kasar Cuba ta tura likitoci Italiya domin taimaka wa kasar tinkarar wannan matsala.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu