Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da coronavirus ta kashe a Italiya ya kusan 800

Hukumomin kasar Italiya sun sanar da cewar yau mutane 793 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus, abinda ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 4,825, yayin da adadin duniya ya zarce 12,000.

Mazauna Milan a Italiya da suka fita waje da mayanin Milan fuska don kada su kamu da cutar coronavirus.
Mazauna Milan a Italiya da suka fita waje da mayanin Milan fuska don kada su kamu da cutar coronavirus. RFI/Sabina Castelfranco
Talla

Alkaluman da gwamnatin kasar ta gabatar sun nuna cewar adadin mutanen da suka kamu da cutar ya tashi daga 6,557 zuwa 53,578.

A yankin Lombardy kawai an samu mutane sama da 3,000 da suka mutu, kuma shine kusan kashi biyu bisa uku na mutanen kasar da suka rasa rayukan su, yayin da aka samu mutane 50 a yankin Lazio da ya hada da birnin Rome.

Hukumar kula da lafiya ta kasar ta bayyana cewar akasarin wadanda suka kamu da cutar masu yawan shekaru ne da ya haura 60.

Yan sanda sun fara bi tituna suna kama wadanda basu da izinin fita ana hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.