An dage shari'ar Fillon a Faransa
Kotu a Faransa ta dage shari’ar da aka shirya farawa tsohon Firaministan kasar Francois Fillon wanda ake tuhuma da laifin almuzzaranci da dukiyar gwamnati wajen biyan matar sa makudan kudade ba tare da aikin komai ba.
Wallafawa ranar:
Fillon da uwargidan sa Penelope sun halarci zaman kotun tare da rakiyar Yan Sanda amma kuma sai suka bukaci dage zaman kotun zuwa ranar laraba domin goyan bayan lauyoyin kasar dake yajin aiki.
Masu bincike na zargin Fillon da sanya sunan uwargidan sa a matsayin masu taimaka masa a Majalisa, tsakanin shekarar 1998 zuwa 2013, inda ake biyan ta euro 10,000 ba tare da tayi aikin komai ba.
Bankado wannan labari na daga cikin batutuwan da suka yiwa tsohon Firaministan tarnaki a yunkurin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2017.
Fillon yaki amincewa da zargin da ake masa, inda yace uwargidan sa Penelope ta masa aiki a mazabar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu