Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Faransa ta amince da sabon tsarin haraji kan mawadata

‘Yan Majalisar Faransa sun mara baya ga wani tayin gwamnati da zai tilastawa shugabannin manyan kamfanonin kasar bayyana yawan kudaden shigarsu matakin da ke matsayin wani bangare na kudirin dokar da ke neman ganin mawadata na biyan adadin harajin da ya kamata.

Majalisar zartaswar Faransa.
Majalisar zartaswar Faransa. Philippe LOPEZ / AFP
Talla

A cewar ministan kasafin kudin kasar ta Faransa Gerald Darmanin, kudirin zai shafi akalla shugabannin dubu 1 da 500 daga kamfanonin kasar 765 wadanda ke samun jumullar kudin da ya haura yuro miliyan 250.

Kudirin wanda ake saran ya fara aiki a cikin kasafin kudin kasar na 2020 wanda majalisar Dattijai ke gab da amincewa da shi, minista Gerald ya ce zai kawo karshen alfarmar da mawadata ke samu na kin biyan harajin da ya cancanta sabanin matalauta da ke biyan yadda doka ta tanada.

A cewar Gerald Darmanin ministan kasafin kudin na Faransa, duk da cewa galibin al’ummar kasar na biyan haraji yadda doka ta tanada amma wasu tsiraru galibi shugabannin manyan kamfanoni na kaucewa biyan na su harajin, wanda kuma ke matsayin babban gibi ga bangaren harajin kasar.

Sabon kudirin gwamnatin dai ya biyo bayan fusatar da Faransawa suka yi bayan matakin gwamnati na yunkurin kwaikwayon tsarin kasashen Belgium da Switzerland wajen rangwantawa mawadata kudaden haraji.

Wani rahoto dai ya nuna yadda attajiran Faransawa kan nemi katin zama a wata kasa don kaucewa biyan makudan kudaden haraji ciki kuwa har da Bernard Arnaut shugaban kamfanin LVMH da Jarumi Ferard Depardieu baya ga shugaban rukunin kamfanin Renault Carlos Ghosn wanda yanzu haka ke fuskantar tuhuma kan halasta kudaden haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.