Maduro ya fito bainar jama'a karon farko cikin watanni 4
Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya fito cikin jama’a karon farko a jiya Asabar, tun bayan halartar bikin faretin sojin kasar a shekarar bara, lokacin da yace an yi yunkurin hallaka shi, a harin bam da aka kai a filin faretin.
Wallafawa ranar:
Maduro a bayyana ga dubban magoya bayansa ne a birnin Caracas domin bikin tunawa da kafuwar gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Venezuela Hugo Chaves.
Rabon da aga shugaba Maduro a bainar Jama’a dai tun ranar 4 ga watan Agustan bara da akai yunkurin halaka shi, wanda kawo yanzu aka kama mutane 30 ciki har da manyan hafsoshin sojin Venezuela 2 da kuma wani mataimakin jagoran ‘yan adawar kasar.
Bayyanar Maduro ta zo dai dai da zanga-zangar da ke gudana a sassan kasar, ta dubban magoya bayan jagoran ‘yan adawa Juan Guaido dake samun goyon bayan kasashen turai, bayan ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu