Isa ga babban shafi
Venezuela

Jagoran 'yan adawa ya bukaci sabuwar zanga-zangar kin jinin Maduro

Jagoran ‘yan adawar Venezuela da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa Juan Guaido, ya bukaci ilahirin magoya bayansa su gudanar da zanga-zanga mafi girma a tarihin kasar, a wani sabon yunkuri na tilastawa shugaba mai ci Nicolas Maduro yin murabus.

Jagoran 'yan adawa a Venezuela Juan Guaido da ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa, yayin ganawa da 'yan Jaridu a birnin Caracas.
Jagoran 'yan adawa a Venezuela Juan Guaido da ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa, yayin ganawa da 'yan Jaridu a birnin Caracas. AFP/Federico Parra
Talla

Kiran na Guaido ya zo ne yayinda a karshen makon nan, wa’adin da manyan kasashen Turai da suka baiwa shugaba Maduro na sake shirya sabon zaben shugaban kasa ke karewa.

Kasashen dai sun yi barazanar bin sawun Amurka, Brazil da wasu kasashen Latin, wajen amincewa da Juan Guaido a matsayin sabon shugaban Venezuela har zuwa lokacin da za’a yi sabon zaben shugaban kasa sahihi.

A ranar Alhamis majalisar Kungiyar Kasashen Turai EU, ta kada kuri'ar goyon bayan jagoran 'yan adawar Venezuela Juan Guaido a matsayin sabon shugaban kasa, yayin da kuma ta bukaci ilahirin kasashen nahiyar da su goyi bayan matakin.

'Yan Majalisar Kungiyar Kasashen Turan 439 ne suka goyi bayan sabuwar gwamnatin jagoran ‘yan adawar, yayin da 104 suke adawa da matakin.

Majalisar ta bukaci baki dayan kasashe 27 da ke karkashin kungiyar ta EU, su amince da  Guaido a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar Venezuela har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaben shugaban kasa, karbabbe ga kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.