Isa ga babban shafi
Jamus-CDU

Angela Merkel ta bukaci jajircewar sabuwar jagorar Jam'iyyar CDU

Jam’iyyar da ke mulkin kasar Jamus ta Christian Democratic Union, CDU ta zabi Annegret Kramp-Karrenbauer a matsayin sabuwar shugaba domin maye gurbin Angela Merkel da ta sauka daga jagorancin bayan kwashe shekaru 18.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a jawabanta bayan murabus ta bukaci jajircewa duk wadda za ta gaje ta don kare manufofin jam'iyyar ta CDU.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a jawabanta bayan murabus ta bukaci jajircewa duk wadda za ta gaje ta don kare manufofin jam'iyyar ta CDU. REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Sabuwar shugabar Anngret Kramp-Karrenbauer ta samu kuri’u 517 daga cikin kuri’u 999 da wakilan Jam’iyyar suka kada domin kada abokin karawar ta.

Kramp-Karrenbauer wadda tsohuwar ministar Yankin Saarland ce ta kada Friedriech Merz, wani hamshakin attajiri wajen samun shugabancin Jam’iyyar, sakamakon kuri’u 482 da ya samu a zaben zagaye na biyu.

Da ta ke jawabi gaban wakilan jam’iyyar, gabanin kada kuri'ar a yau Juma'a bayan matakin ajje mukamin, Angela Merkel ta jaddada cewa lallai jam’iyyar ta samu nasara a karkashin jagorancinta, la'akari da manyan nasarorin da ta samu karkashin jagorancinta har sau hudu.

Merkel cikin jawaban na ta da ta gabatar wanda da dama daga cikin mambobin ke zubda hawaye rike da allunan da ke cewa 'mun gode miki shugabar mu' ta ce ta yi iyakar kokarinta wajen mutunta manufofin jam’iyyar a tsawon shekaru 18 da ta yi tana jagoranci.

Haka zalika Merkel ko bayan kada nasarar Anngret Kramp-Karrenbauer wadda ta fafata da Friedriech Merz wajen neman mukamin jagorancin Jam'iyyar ta CDU, ta ce duk runtsi ka da sabuwar jagorar ta manta da manufofin jam’iyyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.