Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta tsawaita wa'adin binciken iyakokinta

Kasar Faransa za ta tsawaita wa’adin bincikenta akan iyakokinta da kasashen Turai da ke yankin Schengen har zuwa karshen wataan Oktoba mai zuwa saboda tsanantar barazanar ayyukan ta’addanci.

Faransa ta tsawaita wa'adin binciken iyakokinta da kasashen Schengen saboda barazanar tsaro
Faransa ta tsawaita wa'adin binciken iyakokinta da kasashen Schengen saboda barazanar tsaro Reuters/路透社
Talla

Hukumar Gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai ta ce, ta samu sanarwa daga gwamnatin Faransa a cikin wannan makon game da matakinta na tsawaita bincike akan iyakokinta da kasashen Schengen saboda barazanar ayyukan ta’addanci.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake saran cewa a ranar 30 ga wannan wata na Afrilu ne wa’adin bincike kan iyakokin zai kawo karshe, abin da ke nufin cewa, yanzu haka Faransan ta tsawaita wa’adin da watani shida.

Gwamnatin kasar dai ta kaddamar da binciken iyakokin ne tun bayan da kungiyar ISIS ta kai ma ta mummunan hari tare da kashe mutane 130 a cikin watan Nuwamban 2015 a birnin Paris.

Sai dai duk bayan watanni shida, gwamnatin kasar na tsawaita wa’adin saboda yadda ta ke ci gaba da fama da barazanar hare-hare.

Kimanin kasashen Turai 26 ne da suka hada da kasashe mambobin EU 22 ke yankin Schengen, in da suke tsallakawa cikin kasashen juna ba tare da fasfo ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.