Isa ga babban shafi
Faransa

Ana zargin kamfanin Larfarge da yin alaka da ISIS

Kamfanin hada siminti na Lafarge, ya ce jami’an bincike na kasar Faransa, sun kai samame a ofisoshinsa, domin neman bayanai da ke alakanta kamfanin da kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Syria, musamman IS.

Wani bangare na ginin kamfanin siminti na Larfarge da ke birnin Paris a kasar Faransa.
Wani bangare na ginin kamfanin siminti na Larfarge da ke birnin Paris a kasar Faransa. Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

Mai Magana da yawun kamfanin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa, ana yin binciken ne domin tantance sahihancin rahoton da wani gidan rediyo ya bayar a kan zargin.

Tun a cikin watan Yuni, wasu alkalai a Faransa, suka fara bincike kan rahoton da ya ce, kamfanin simintin na Lafarge, ya tura kudade ga wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a Syria, daga cikinsu kuma har da kungiyar IS.

Rahoton ya ce kamfanin ya yi haka ne, domin ya samu damar cigaba da ayyukansa a arewacin kasar ta Syria, duk da irin rikicin da kasar ke fama da shi.

Rahoton da ya bulla a bara, ya ce kudaden da kamfanin simintin ya biya kungiyoyin a Syria kudi sun kama daga dala dubu 80, zuwa dala dubu 100, domin samar da tsaro ga ma’aikatansa a tsakanin shekarun 2013 da 2014, kuma aka rawaito cewa IS ta samu kason dala dubu 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.