Isa ga babban shafi
Ingila

Salman Abedi da ake zargi ya kai harin Manchester

‘Yan sanda a Birtaniya na tsare da mutane 7 yanzu da ake zargin na da alaka da Maharin Manchester Salman Abedi wanda aka bayanna cewa iyayensa ‘yan asalin Libya ne.

Salman Abedi, dan asalin Libya da ake zargi ya kai harin Manchester
Salman Abedi, dan asalin Libya da ake zargi ya kai harin Manchester metrouk2
Talla

Ko wanene Salman Abedi
An haifi Salman Abedi a shekarar 1994 a birnin Manchester na Birtaniya, bayan iyayensa sun tsere daga Libya saboda mulkin marigayi Kanal Gaddafi.

Iyayensa sun shafe tsawon shekaru a birnin London, abin da ya bai wa mahaifinsa daman zama ladani a masallacin birnin.

Abedi ya halarci makarantar maza da Burnage tsakanin 2009-2011 a birnin, kazalika ya hallarci kwallajin Manchester a 2013 kafin ya je Jami’ar Salford a 2014.

Sai dai ya ajiye karatun daga baya, inda ya koma aiki a wani gidan beredi dake birnin, kuma kamar yadda rahotanni ke nuni an sha gargadi hukumomin kan tsatsauran ra’ayinsa.

Abokansa sun shaida cewa Maharin yana sha’awar kwallon kafa domin masoyi kungiyar Manchester United ne.

Salman na da ‘yar uwa mace da maza biyu.

A kwanankin baya iyayensa sun koma zaman Libya, sai dai daga baya Abedi ya dawo Ingila bayan tsawon lokaci.

Ana dai cigaba da zurfafa bincike domin sanin hakikan wadanda suka taimakawa Abedi duk da cewa akwai rahotanni da ke cewa ya jima yana alaka da mayakan IS da ke Libya kafin wanann harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.