Isa ga babban shafi
Faransa

Tsugunno bata karewa Emmanuel Macron ba

Sunayen mutane 428 da gungun dake goyon bayan zababben shugaba kasar Faransa Emanuel Macron, (La Républic en Marche ya gabatar, na ‘yan takarar kujerun majalisar dokokin kasar bai samu amincewar jam’iyar du Modem mai kawance ba.

Zababben shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Francois Bayrou, jagoran jam'iyyar kawance ta (MoDem), yayin ganawa da magoya baya.a ranar 12 ga watan Afrilu da ya gabata.
Zababben shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da Francois Bayrou, jagoran jam'iyyar kawance ta (MoDem), yayin ganawa da magoya baya.a ranar 12 ga watan Afrilu da ya gabata. REUTERS/Regis Duvignau
Talla

Bayan korafin da aminiyar kawancen gungun na La République en marche, jam’iyar Modem ta yi, babban sakataren 'Emmanuel Macron, Richard Ferrand, ya ce ba abin tada hankali bane komai zai tafi kamar yadda ya dace.

Fallasa jerin sunayen ‘yan takarar da jam’iyar ta Emmanuel Macron ta yi, a zaben ‘yan majalisar dokoki bai samu amincewar abukiyar kawancenta Modem ba, a wata makala da ta fito a jaridar Observateur shugabanta François Bayrou ya ce, jerin sunayen ‘yan takarar da aka gabatar na nuni da cewa bata canza zani ba, domin kuwa ‘yan socialist ne suka maimaita

A ganinsa dai wadannan sunayen da aka gabatar ‘yan socialiste zalla ne, a yayinda tasa jam’iyar aka ci gari da ita aka barta da kuturun bawa, da ‘yan takarar da basu taka kara suka karya ba.

Magajin garin ya kara da cewa ba’a mutunta tsarin yarjejeniyar da suka cimma da jam’iyyar ta la République en marche ba.

Bayan da ya ce da farko sun amince kan fitar da ‘yan takarar tare, sai gashi an kewaye shi, wannan ya kai François Bayrou ga yin gori inda yake cewa a lokacin da ya marawa Emanuel Macron baya ya na da kashi 18% ne kawai. Dan haka su suka sa aka zabe shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.