Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Birtaniya: Kan mambobin Tarayyar Turai a hade ya ke

Mambobin Tarayyar Turai sun ce kan su a hade ya ke a yayin da shugabannin kasashen ke shirin gudanar da taro domin amincewa da sharuddan tattaunawar ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Firaministan Birtaniya Theresa May
Firaministan Birtaniya Theresa May REUTERS/Neil Hall
Talla

Jagoran tattauna batun ficewar Birtaniya na kungiyar Tarayyar Michel Bernier ya ce kan mambobin kungiyar a hade ya ke kuma a shirye suke game da soma tattauna ficewar birtaniya daga kungiyar.

Amma mataimakin Firaministan kasar Malta da ke rike da ragamar shugabancin kungiyar ta Tarayyar Turai na karba karba ya ce dole su kare bukatun kungiyar, kuma kansu a hade yake akan bukatun.

Firaministan Birtaniya Theresa May ta zargi mambobin kasashen da shirin adawa da bukatar ficewar kasar daga kungiyar, kalamanta kuma na zuwa bayan shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kada Birtaniya ta yi tunanin ficewarta Tarayyar Turai kuskure ne.

A karshen makon nan ne ake sa ran shugabannin kungiyar za su gana domin amincewa da sharrudan soma tattaunar ficewar.

A ranar 22 ga Mayu ne ake sa ran soma tattaunawar, kodayake sai an kammala zaben Birtaniya da za a gudanar 8 ga Yuli kafin shiga tattaunawar gada gadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.