Isa ga babban shafi
Faransa

Philippe Poutou dan takarar zaben 2017 a Faransa

Philippe Poutou, daya daga cikin mutane 11 da za su fafata da juna a zaben shugabancin kasar Faransa na shekarar 2017, wanda za’a yi zagayen farko a ranar 23 ga watan Afrilu.

Dan takarar shugabancin Faransa a shekara ta 2017, Philippe Poutou.
Dan takarar shugabancin Faransa a shekara ta 2017, Philippe Poutou. REUTERS/Lionel Bonaventure
Talla

TARIHIN PHILIPPE POUTOU

An haifi Philippe Poutou a ranar 14 ga watan Maris a shekarar 1967 a birnin Villmomble, a Seine-sain-Denis.

Ma’aikacin kamfanin kera motocin Ford, Philippe Poutou ya dauki hutun makonni biyar don yin kamfain a kokarinsa na zama shugaban kasar Faransa.

A baya can Poutou ya taka muhimmiyar rawa a yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin na Ford wajen hana korarar ma’aikata 2000 daga bakin aikinsu.

Philippe Poutou na jam’iyyar dake adawa da jari hujja, ya soma samun karbuwa a yayin mahawarar da aka tafka a tsakaninsa da ‘yan takarar 10 makwanni uku kafin soma zaben zagaye na farko, inda dukkan 'yan takarar suka yi kokarin su bayyana manufofinsu,

Poutou ya dusashe hasken taurarin sauran ‘yan takara ta hanyar sukar manufofinsu da zafafan kalamai musamman ‘yan takarar da ake zargi da laifin rashawa, al’amarin da ya yi matukar jan hankulan jama’ar kasar.

A shekarar 2012 ma dai dan Poutou ya tsaya takara inda ya sami kashi daya cikin kuri’un da aka kada, a wannan karon ma dai bai zarta hakan sai dai dan takarar ya kara samunn karbuwa daga jama’a bisa kalamansa na tsaga gaskiya komai dacinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.