Isa ga babban shafi
Sweden

An cafke Direban da ya kashe mutane a Stockholm

An cafe wani mutumin da ake zargi da ta’addanci a Sweden bayan kutsa kai da babbar mota a cikin taron jama’a a tsakiyar birnin Stockholm.

'Yan sanda na ba da tsaro bayan harin Stockholm
'Yan sanda na ba da tsaro bayan harin Stockholm REUTERS/Daniel Dikson
Talla

‘Yan sanda sun tabbatar da cewa mutane 4 aka kashe tare da raunanta 15 sakamakon taka su da aka yi da mota, tare da zurfafa bincike a game da lamarin.

A cewar masu gabatar da karar an cafke, Karin Rosander, wanda ga duk kan alamu harin da ya kai na da alaka da ta’addanci.

Shugabanin kasashen duniya na ci gaba da yin Allah-wadai da wannan al’amari da yanzu haka ya matukar girgizar al’ummar kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.