Isa ga babban shafi
Faransa

An kai hari a Ofishin asusun bayar da lamuni a Paris

Mutum daya ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu da aka kunshe a wasika da aka tura wa babbar cibiyar Asusun bayar da Lamuni ta Duniya IMF da ke birnin Paris na Faransa a yau alhamis.Bayan fashewar dai ne , jami’an tsaro suka bukaci jama’a su fice daga cikin ginin domin gudanar da bincike. 

Ofishin asusun bayar da Lamuni na IMF da ke Paris na kasar Faransa
Ofishin asusun bayar da Lamuni na IMF da ke Paris na kasar Faransa 路透社REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Hukumomin kasar sun sanar da tura yan Sanda  a unguwar domin  karfafa tsaro dama maida hankali wajen gudanar da bicinke a kai.

Da jimawa hukumomin na Faransa suka sanar da daukar matakan da suka dace na tsaro a birane kamar su Paris dama wajejen shakatawa.

Ya zuwa yanzu  ana ci gaba da gudanar da bicinke domin tanttance ainayin abinda ya faru a ofishin asusun bayar da lamuni dake Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.