Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan Sanda sun kai samame a gidan Fillon a Paris

Jami’an ‘yan sanda sun kai samame a gidan dan takaran shugabancin Faransa Francois Fillon saboda badakalar nan ta aikin boge da ta dabaibaye shi.

François Fillon na cikin tsaka mai wuya
François Fillon na cikin tsaka mai wuya REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Ana zargin Fillon na jam’iyyar masu ra’ayin rikau da bai wa matarsa makuden kudade karkashin wani aikin boge, yayin da daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar, Dominique de Villepin ya gargade shi game da raba kawunan ‘yan jam’iyyar.

A ranar Alhamis ne jami’an ‘yan sandan suka kai samame a gidansa da ke birnin Paris, kuma a dai dai lokacin da ya isa kudancin Faransa don yakin neman zabe.

Sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani game da sakamakon samamen, yayin da tawagar yakin neman zabensa ta tabbatar aukuwar lamarin.

A ranar Laraba ne Mr. Fillon ya ce, a shirye yake ya fuskanci tuhuma game da zargin sa da biyan mai dakinsa da ‘ya'yansa dubban kudi na Euro a karkashin aikin boge a majalisar dokokin kasar.

Duk da wannan zargin dai, Mr. Fillon ya lashi takobin ci gaba da yakin neman zaben don ganin ya samu kujerar shugabancin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.