Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan takarar shugabancin Faransa 2 za su gurfana gaban Kotu

Ma’aikatar Shari’ar Faransa ta ce babu abinda zai hana ta gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa manyan ‘yan takaran shugabancin kasar biyu, Francois Fillon da Marine Le Pen kafin zaben da za’ayi a watan Afrilu.

Faransa za ta gudanar da zaben shugabancin kasar a watan Afrilu
Faransa za ta gudanar da zaben shugabancin kasar a watan Afrilu REUTERS/Philippe Wojazer/Benoit Tessier/Robert Pratta
Talla

‘Yan takarar biyu na fuskantar zarge zarge karbar kudi daga Majalisar kasashen Turai ta hanyar da bata kamata ba, da kuma biyan ma’aikata na bogi daga asusun Majalisar Faransa.

Alkalin alkalan Faransa Jean-Jacques Urvoas ya ce babu yadda za su kauda kan su wajen gudanar da bincike kan zarge zargen saboda karatowar lokacin zabe, domin wannan babban kalubale ne dake fuskantar bangaren shari’a.

Mai shari’a Urvoas yayi watsi da zargin cewar yana samun matsin lamba daga shugaban kasa Francois Hollande kamar yadda bangaren Francois Fillon yayi zargi.

Jami’in yace babu nuna san kai wajen binciken ‘yan takaran biyu wadanda ke cikin na gaba gaba wajen lashe zaben shugaban kasar, zagaye na farko.

Francois Fillon wanda ake gani kamar zai iya zama shugaban kasa na gaba, ya gamu da suka sakamakon binciken da ya nuna cewar ya biya matar sa da ‘ya’yan sa albashin bogi ba tare da aiki ba, yayin da ita Marine Le Pen aka bankado cewar ta karbi kudi daga Majalisar Turai da sunan jami’an ta alhali suna karbar albashi a Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.